Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta bukaci dakatar da jarabawar da ake gudanarwa a dukkan cibiyoyin Makarantar Koyon Shari’a ta Najeriya, sakamakon zargin cin zarafi da hana dalibai mata Musulmi masu sanya hijabi shiga dakunan jarabawa.
Kungiyar ta kuma bukaci gudanar da bincike kan lamarin, wanda ta ce ya faru a ranar Asabar, 31 ga Oktoban 2026, lokacin jarabawar karshe ga daliban da ke neman shiga aikin lauya.
A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar ranar Lahadi, ya ce an hana wasu dalibai mata masu hijabi shiga dakunan jarabawa a wasu cibiyoyin makarantar.
Ya ce a wasu wuraren an tilasta wa daliban tsayawa a wajen dakunan jarabawar na kusan awa guda, kafin daga bisani aka ba su damar shiga bayan sun cire hijabinsu.
Akintola ya ce kungiyar ta samu kiran waya da sakonnin korafi daga daliban da abin ya shafa, iyayensu da sauran Musulmi.
Ya bayyana lamarin a matsayin tauye hakkin dalibai na neman ilimi da gudanar da addininsu, yana mai cewa abin da ya faru ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
MURIC ta yi nuni da sashe na 38 da 42 na kundin tsarin mulkin 1999, wadanda suka tanadi ‘yancin addini da kariya daga nuna bambanci.
Ta kuma ambaci hukuncin Kotun Koli na shekarar 2022 kan shari’ar gwamnatin jihar Legas da Asiyat Abdulkareem, wadda ta ce ya tabbatar da ‘yancin dalibai mata Musulmi na sanya hijabi.
Kungiyar ta yi barazanar shirya zanga-zangar lumana a cibiyoyin makarantar fadin kasar idan ba a biya bukatunta ba.
Ya zuwa lokacin fitar da sanarwar, Makarantar Koyon Shari’a ta Najeriya ba ta mayar da martani kan zarge-zargen ba.