Tinubu Ya Sake Jaddada Kudirinsa Na Ci Gaban Najeriya Bayan Addu’a A Cikin Ka’aba

0 22

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada kudirinsa na ci gaban kasa, yana mai cewa zai ci gaba da aiwatar da manufofin da za su bunkasa tattalin arziki da samar da damarmaki ga matasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne bayan kammala Umrah a kasar Saudiyya, inda aka ba shi dama ta musamman ta shiga cikin dakin Ka’aba da ke Makka domin gudanar da addu’a tare da tawagar Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, shugaban ya gode wa Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz Al Saud, da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa wannan dama.

Tinubu ya ce ya yi amfani da damar wajen rokon Allah ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da yi wa al’ummar Najeriya hidima, yana mai cewa ya yi imanin an amsa addu’arsa.

Ya kuma yi nuni da ayar 26 ta Suratul Ali-Imran, wadda ta bayyana cewa Allah ne kadai ke bayar da mulki da karbe shi a lokacin da ya so.

Shugaban ya bayyana mulki a matsayin amana daga Allah, wadda ya kamata a yi amfani da ita wajen yi wa al’umma hidima cikin gaskiya da rikon amana.

Dangane da tattalin arziki, Tinubu ya bayyana kyakkyawan fata kan halin da kasar ke ciki, yana mai cewa an samu ci gaba kuma an kafa tubalin farfadowar tattalin arziki.

Ya kuma jaddada muhimmancin zuba jari a makomar matasa, yana mai cewa matakan da shugabanni ke dauka a yanzu za su shafi makomar al’ummomi masu zuwa.

Daga cikin tawagar shugaban akwai Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da gwamnonin jihohin Borno, Sokoto, Jigawa, Kaduna, Yobe da Kwara.

Haka kuma, shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdulsamad Rabiu, da shugaban kamfanin Oando, Wale Tinubu, na cikin wadanda suka raka shugaban.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner