Na roki Allah Ya Ba Ni Hikimar Jagorantar Najeriya Kafin Zaben 2023 – Tinubu

0 20

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya roki Allah ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da yi wa al’ummar kasar hidima, yana mai cewa ya yi irin wannan addu’a kafin zaben shugaban kasa na 2023.

Tinubu ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Litinin, bayan gudanar da addu’a a Masallacin Harami da ke Makka, kasar Saudiyya.

Shugaban ya ce yana godiya ga Allah bisa ba shi damar gudanar da ibadar Umrah cikin koshin lafiya.

Ya bayyana cewa daya daga cikin addu’o’insa ita ce Allah ya mayar da bambancin addinai da al’adu da ke Najeriya zuwa arziki da ci gaba ga kasa.

Tinubu ya ce ya roki Allah ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da jagorantar al’umma, yana mai cewa ya yi imanin an amsa addu’arsa.

Ya kuma bayyana cewa kafin zaben 2023 ya gudanar da irin wannan ibada, inda ya roki Allah ya saukaka masa Umrah, tare da alkawarin dawowa domin gode masa idan ya samu nasara.

Shugaban ya ce samun damar jagorantar Najeriya wata ni’ima ce daga Allah, yana mai jaddada cewa mulki amana ne da ya kamata a yi amfani da shi yadda ya dace.

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su fifita tsoron Allah, su bi lamirinsu tare da zabar hanyar da za ta kai kasar ga ci gaba.

Dangane da tattalin arziki, Tinubu ya ce Najeriya na samun sauki daga mawuyacin halin da ta shiga, yana mai cewa tubalin da gwamnatinsa ta kafa yana da karfi, kuma ya kamata a ci gaba da zuba jari a makomar matasa.

Ya kuma gode wa hukumomin Saudiyya bisa ba shi damar shiga cikin dakin Ka’aba, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin tarihi.

Shugaban ya ce yana da yakinin cewa Najeriya za ta shawo kan kalubalen da take fuskanta ta hanyar dogaro da Allah.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner