A makoman nan ne kadinal daga sassa daban-daban za su taru a Vatican domin zaben sabon Paparoma

0 460

A wannan makon, cardinal-kadinal daga sassa daban-daban na duniya za su taru a Vatican domin gudanar da sahihin zaɓen sabon Paparoma, wanda zai maye gurbin marigayi Paparoma Francis, wanda aka yi masa jana’iza a ranar 26 ga watan Afrilu.

Zaɓen, wanda ake sa ran zai fara bayan ranar 7 ga Mayu a cikin dakin Sistine Chapel, zai gudana cikin sirri ba tare da amfani da waya, da intanet ko fita ba har sai an fitar da sunan sabon shugaban cocin Katolika.

Duk da babu kamfe a fili, ana hasashen wasu cardinal din da suka haɗa da Cardinal Tagle daga Philippines, da Parolin daga Italiya, da Turkson daga Ghana da Erdo daga Hungary – inda bambance-bambancen ra’ayi tsakanin masu sauyi da masu ra’ayin gargajiya ke nuna ƙalubalen zaɓen.

Alamun hayaki fari daga bututun Sistine Chapel ne zai nuna an zaɓi sabon Paparoma, yayin da hayaki baki ke nuni da rashin cimma matsaya.

Leave a Reply