A yau Alhamis, APC ta shirya taron tabbatar da Umar Namadi a matsayin ɗan takarar gwamna na 2027 a jihar Jigawa
Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa za ta yi babban taron tabbatar da Gwamna Umar Namadi a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar domin sake tsayawa takara karo na biyu a zaɓen shekarar 2027.
Sanarwar taron ta fito ne ta bakin Shugaban APC na Jihar Jigawa, Hon. Ahmad Garba MK, inda ya ce za a gudanar da taron a yau ranar Alhamis da misalin ƙarfe 2:00 na rana a Filin Wasanni na Dutse da ke kan hanyar Shuwarin.