Matasa ‘yan soshiyal midiya masu rubuce-rubucen tallata jam’iyyar PDP da Gwamnatin Jihar Zamfara a kafafen sada zumunta sun ayyana yajin aiki, tare da dakatar da duk wani wallafa bayanai ko tsokaci da ya shafi gwamnati da jam’iyyar – har zuwa wani lokaci.
Matakin ya biyo bayan wata sanarwa da jagorancin Gamayyar Kungiyar Marubutan Social Media na PDP a Zamfara ya fitar. A cewar sanarwar, matakin na zuwa ne bayan wani nazari da ƙungiyar ta gudanar kan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi tsarin cikin gida da kuma tabbatar da tsari a ayyukansu.
Kungiyar ta umurci dukkan ’yan kungiyar da su dakatar da duk wani rubutu ko aiki da zai saba wa wannan mataki, har sai an fitar da sabon umarni.
Sanarwar ta ƙara da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da sanar da jama’a da mambobinta duk wani sabon ci gaba ko sauyi da zai taso daga matakinda suka dauka.