Abdulaziz Yari ya samar da manyan motocin takin zamani 76 ga manoma a matsayin tallafi

0 174

Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya samar da manyan motocin takin zamani 76 da za a raba su ga manoma tare da zaftare kashi 50 cikin 100 na farashinsa a matsayin tallafi. 

Ibrahim Muhammad, shugaban kwamitin yada labaransa ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a jiya a garin.

A cewar sanarwar, shugaban kwamitin, Alhaji Lawal Liman ne, ya bayyana hakan a wani taro da mambobin kwamitin rabon takin.

Ya bayyana cewa, kowane daga cikin kananan hukumomi takwas na gundumar Zamfara ta Tsakiya da Arewa za su karbi manyan motocin takin guda biyar.

Sanarwar ta ce yankuna shida na gundumar Zamfara ta Yamma da Sanatan ke wakilta, kowanensu zai karbi manyan motocin takin zamani shida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: