Gwamnatin tarayya ta ceto wasu mutane 7 da suka makale a wajen hakar ma’adanai dake jihar Neja

0 132

Gwamnatin tarayya ta ceto wasu mutane bakwai da suka makale a wani wajen hakar ma’adanai a yankin Galadima Kogo da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Ministan ma’adanai, Dele Alake ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Tomori ya fitar jiya Talata a  Abuja.

Ya ce tuni aka tura masu bayar da agaji zuwa wajen da lamarin ya faru, inda ya kara da cewa ana aikin ceton tare da hadin gwiwar kamfanin hakar ma’adanai.

Kamfanin dillancin labaran na kasa (NAN), ya ruwaito cewa mutane 30 ne, suka makale cikin ramin da ake hakar ma’adanai da kamfanin African Minerals and Logistics Ltd ke aiki.

NAN ya kara da cewa, Alhaji Abdullahi Arah, Darakta-Janar na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar Neja ya ce lamarin ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: