Abubakar Fulata ya kashe kudi kimanin Naira miliyan 1,000 wajen aiwatar da ayyukan mazabun sa a 2021

0 77

Wakilin mazabar Guri da Kirikasamma da Birniwa a majalissar wakilai ta kasa Dr Abubakar Hassan Fulata yace ya kashe kudi kusan naira miliyan 1,000 wajen aiwatar da ayyukan mazabu a bara.

Dr Abubakar Hassan Fulata ya sanar da haka ne a lokacin ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jiha.

Yace wasu aiyukan an kammala yayin da wasu suke daf da kammaluwa.

Dr Abubakar Hassan Fulata ya kara da cewar ayyukan mazabun da ya aiwatar na 2021 sun hadar da samar da naurorin samar da ruwan sha masu amfani da hasken rana a garuruwan Bulama Malun da Munkawo da Makintari da Matarar Malinta da Arin da kuma Madamuwa.

Yace an tona fanfunan tuka tuka guda 8 a kowacce karamar hukuma ta mazabarsa, yayin da ya bayar da aikin hanyar motar Marma zuwa Dawa kan kudi naira miliyan 100.

Dr Abubakar Fulata ya kuma ce an fara sanya kwalta akan hanyar Madamuwa zuwa Lafiya da ake ginawa kan kudi naira miliyan 100 yayin da za a fara aikin hanyar Lafiya zuwa Arin zuwa  cikin garin Guri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: