Gwamnatin Tarayya ta ce ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda ya taimaka wajen yaki da rashin tsaro

0 100

Gwamnatin Tarayya ta ce ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda ya taimaka wajen yaki da rashin tsaro.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana haka a jiya a lokacin da ya ziyarci babban ofishin kamfanin Media Trust dake wallafa jaridar Daily Trust da Aminiya.

Ya ce ayyanawar ta halasta amfani da muggan makamai wadanda kafin ayyanawar ba zai yiwu ba.

Ministan ya bayyana damuwarsa game da yadda ake samun yawaitar kashe-kashen matsafa a kasar nan, yana mai cewa gwamnati na duba sabbin matakan da za a dauka na daidaita shafukan sada zumunta saboda masu laifin na amfani da su a matsayin wata kafar samun kwarin guiwa kan ayyukansu.

Ya ce gwamnati za ta fara wayar da kan jama’a kan illolin kashe-kashen matsafa, wanda hukumar wayar da kan jama’a za ta jagoranta; yayin da hukumar tace fina-finai ta kasa za ta tantance fina-finan da aka yi akan haka.

Ya kuma bayyana cewa, kasar China ta daina baiwa Najeriya lamuni saboda rahotannin da ke cewa kasar za ta fada kangin fatara nan ba da dadewa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: