Gwamnatin jihar Jigawa ta bayar da umarnin murkushe ayyukan kungiyar taskforce

0 64

Gwamnatin jihar Jigawa ta bayar da umarnin murkushe ayyukan kungiyar taskforce masu shigo da kayayyaki daga kasashen waje ta kasa bisa yadda kungiyar ke gudanar da harkokinta ba bisa ka’ida ba.

Wata sanarwa da daraktan ayyuka na musamman na jiha, Alhaji Yusuf Muqaddas ya fitar, yace gwamnati ta lura cewa kungiyar wacce aka kafa da nufin shawo kan matsalar bazuwar kananan makamai a cikin al’umma yanzu haka ta karkatar da ayyukanta zuwa yaudarar matasa cewa za a samar musu ayyukan yi.

Sanarwar ta yi kira ga ma’aikatu da hukumomin gwamnatin da su nesanta kansu da hulda da ayyukan haramtacciyar kungiyar tsaron ta taskforce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: