Dalilan da yasa shugaba Buhari ya gudanar da zaman ganawa tare da gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki

0 73

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a halin yanzu yana gudanar da zaman ganawa tare da gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki.

Ana gudanar da zaman ganawar a zauren majalisar zartarwa dake fadar shugaban kasa a Abuja.

Daga cikin wadanda suke halartar zaman ganawar akwai mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnoni 18, wadanda suka hada da na Jigawa, Yobe, Kano, Kogi, Ekiti, Nasarawa, Kwara, Ebonyi, Lagos, Imo, Ogun, Borno, Niger, Gombe, Osun, Kebbi, Filato tare da mataimakin gwamnan jihar Anambra wanda ya fice daga jam’iyyar APGA zuwa jam’iyyar APC a bara.

Ana gudanar da zaman ganawar sanadiyyar jinkirin da ake samu wajen shirya babban taron jam’iyyar na kasa daga kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar karkashin shugabancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, lamarin dake haifar da zaman dar-dar da rashin sanin makomar jam’iyyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: