Abubakar Malami Da Ministar Kudi Ba Sa Bayar Da Hadin Kai Ga Kwamitin Binciken Batan N2.4Bn

0 54

Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai da ke binciken zargin asarar sama da dala biliyan 2 da miliyan 400 na kudaden da aka samu daga sayar da ganga miliyan 48 ta danyen mai ba bisa ka’ida ba a shekarar 2015, ya koka kan cewa babban Lauyan Tarayya Abubakar Malami da Ministar Kudi, Zainab Ahmed ba sa bayar da hadin kai ga kwamitin.Hakan na zuwa ne yayin da kwamitin ya sake kiran Abubakar Malami da Zainab Ahmed da su gurfana a gabansa da wasu takardu da bayanan da za su taimaka wajen gudanar da aikinsa.Da yake jawabi yayin dawowa zaman kwamitin a yau, shugaban kwamitin, Mark Gbillah ya ce kwamitin ba ya samun hadin kan da ake bukata daga Abubakar Malami da Zainab Ahmed duk da jerin wasikun da aka aika musu.Mark Gbillah ya ce kwamitin da majalisar wakilai ta yiwu su tilasta musu yin amfani da karfin ikonsu na majalisa wajen tilasta wa mutanen biyu da sauran bangarorin da aka gayyata su gabatar da kansu idan suka kasa ba da hadin kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: