Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Shugaban Immigration, Isah Jere Da Yayi Ritaya

0 64

Gwamnatin tarayya ta bukaci shugaban hukumar shige da fice ta kasa, Immigration, Isah Jere da yayi ritaya.
A wata wasika daga hukumar kula da hukumomin civil defence, gidajen gyara da’a, kashe gobara and immigration, mai kwanan watan 17 ga watan Afrilu, wacce kuma aka aika wa shugaban hukumar ta immigration, gwamnatin tarayya ta umurce shi da ya mika mulki ga mafi girman mukami a jami’an hukumar.
Wannan umarni na zuwa ne biyo bayan zargin da aka yi wa shugaban na yin yunkurin sake tsawaita wa’adinsa a mukamin.
Isah Jere ya samu karin wa’adin ritayar sa da shekara guda, daga shekarar da ta gabata zuwa ranar 24 ga watan Afrilun da muke ciki.
Wasu jami’an hukumar sun yi barazanar gudanar da zanga-zanga idan har gwamnatin tarayya ta sake tsawaita wa’adinsa.
Sai dai a cikin wasikar mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren hukumar, Obasi Edozie Edmund, gwamnatin tarayya ta umurce shi da ya mika mulkin a ranar ko kafin ranar Litinin 24 ga watan Afrilun da muke ciki har zuwa lokacin da shugaban kasa zai nada sabon shugaban hukumar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: