Shugaba Buhari Ya Dawo Najeriya Bayan Ziyarar Aiki Ta Kwanaki 8 A Saudiyya

0 54

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan ziyarar aiki ta kwanaki takwas a kasar Saudiyya, inda ya kuma yayi Umrah.
A yau ne shugaban kasar ya bar Saudiyya ta filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz na Jeddah na kasar Saudiyya.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, jami’an gwamnatin Saudiyya da shugabannin gargajiya da na addini daga Najeriya da kuma wasu manyan ma’aikatan ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar sun halarci filin jirgin saman domin bankwana da shugaban.
A halin da ake ciki kuma, shugaban kasar ya mayar da martani kan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke na mayar da Sanata Ifeanyi Ararume a matsayin shugaban Kamfanin Man Fetur na Kasa NNPPC wanda ba zababbe ba.
A jiya ne wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta mayar da Ifeanyi Ararume a matsayin shugaban kamfanin man na NNPPC tare da ba shi diyyar naira biliyan 5.
Shugaban kasar, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina ya fitar a yau, ya nem ayi nazari game da shari’ar Ifeanyi Ararume da Kamfanin Man na NNPPC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: