Karar Harbe-Harben Bindiga Da Rugugin Jiragen Yaki Sun Wargaza Shirin Tsagaita Wuta A Birnin Khartoum Na Kasar Sudan.

0 91

Karar harbe-harben bindiga da rugugin jiragen yaki sun wargaza shirin tsagaita wuta a birnin Khartoum na kasar Sudan.

An sami rahoton fada ya barke a kusa da hedikwatar sojojin da ke kusa da filin jirgin sama a tsakiyar birnin, wanda ke kewaye da gidajen mutane.

Wasu janar-janar guda biyu masu gaba da juna dake rikicin sun amince da dakatar da fadan na sa’o’i 24 domin ayyukan jin kai.

Kusan mutane 200 ne aka kashe a fadan da aka fara a ranar Asabar.

Mazauna birnin na fama da karancin abinci da ruwan sha yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojoji da ‘yan kungiyar RSF.

Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ce babu wata alama da ke nuni da cewa yakin na Sudan zai yi sauki.

Wata mata da ke zaune a birnin Khartoum ta shaida wa manema labarai cewa babu sauran ruwan sha a gidanta.

A Jami’ar Khartoum, an kashe wani dalibi bayan da harsashi ya fada kansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: