Kamfanin gine-ginen China na CCECC ya mika kashin farko na aikin jami’ar Sufuri ga gwamnatin tarayya.
Shugaban kamfanin na CCECC Jason Zhang ne ya mika aikin ga Ministan sufuri na kasa Sanata Sa’id Alkali a Abuja.
Zhang ya ce, a matsayinsa na daya daga cikin manyan ‘yan kasuwa a fannin samar da ababen more rayuwa, mika jami’ar wata shaida ce ta sadaukar da kai ga ayyukan ci gaban jama’a da kuma alkawarin tallafawa ci gaban matasa a Najeriya.
A cewarsa, yana daya daga cikin hanyoyin CCECC na bunkasa Najeriya da kuma taimakawa ci gaban fasaha na kasa.
Ya ce an samar da ayyukan yi sama da dubu daya da kuma shirye-shiryen musayar kudade da dama da aka gudanar a yayin aikin.
Da yake mayar da martani, Ministan Sufuri, Sanata Sa’id Alkali, ya ce jami’ar ba ta da bambanci a tsari, ma’auni, kuma ta cika bukatun Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa, NUC, wanda ya jawo hankalin kafa dokar kafa mai lamba 34 ta shekarar 2022.