Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Dawaki da ke yankin babban birnin tarayya Abuja inda suka sace mutane 13, amma kuma daga bisani jami’an tsaro sun ceto hudu daga cikinsu bayan sun yi artabu.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun fara zuwa ne suka sace mutum hudu, amma mutanen suka tsere, daga bisani kuma suka sake kama mutum 13, a harin wanda aka kai ranar Lahadi da daddare
Bayan sun kama mutanen ne jami’an tsaro suka kai dauki inda suka yi artabu da su a kusa da madatsara ruwa ta Usman Dam, inda sukayi nasarar ceto mutum hudu daga cikin 13.
Sai dai kuma wasu rahotannin na cewa mutanen da aka sace sun kai 20.
Sai dai kuma a wata sanarwa da rundunar ‘yansanda ta Abuja ta fitar, mai magana da yawun rundunar SP Josephineb Adeh ta tabbatar da aukuwar satar mutanen.
Sai dai sanarwar da ‘yansandan suka fitar wadda a ciki suka ce da hadin kai da mafarauta suka yi wa barayin kwanton-bauna a tsaunin Ushafa daga Bwari, ba ta bayyana yawan mutanen da aka sace ba.