“Bai kamata a zargi Bola Tinubu ba kan batun tabarbarewar tattalin arziki” – Ismaeel Ahmed

0 203

Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki, Wani Mamba a  jam’iyyar APC, Ismaeel Ahmed, ya wanke shugaban kasa Bola Tinubu, yana mai cewa bai kamata a zarge shi da tabarbarewar tattalin arzikin kasa ba.

Ahmed, wanda ya kasance bako a wani Shirin Siyasar na Gidan Talabijin na Channels a jiya ya ce, tsare-tsaren da gwamnat ta fito dasu masu tsauri ya zama dole domin farfado da tattalin arzikin kasa.

Shugaban Bola Tinubu ya dauki wasu tsauraran matakai na tattalin arziki da suka hada da cire tallafin man fetur wanda ya haifar da tsadar rayuwa da sufuri.

Jigon na APC ya ce kafin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ‘yan takarar jam’iyyar Labour Peter Obi da takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar suma duk sunyi yi alkawarin kawo karshen tallafin man fetur da kuma gyara tsarin hada-hadar chanjin kudaden kasashen waje.

Leave a Reply

%d bloggers like this: