Fintiri Ya Ce Ya Fafata A Zaben Gwamnan Jihar Da Makiyan Dimokuradiyya Da Suka Hade Masa Kai.

0 84

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ce ya fafata a zaben gwamnan jihar da makiyan dimokuradiyya da suka hade masa kai.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a jiya a yayin wata hira da yayi a gidan Talabijin na Channels, yace masu adawa da shi suna son mace ta zama gwamna ba tare da la’akari da ayyukan sa ba.
Ahmadu Fintiri ya kuma sha alwashin gurfanar da wadanda suka aikata laifuka a lokacin zaben gwamnan a gaban kuliya.
Ahmadu Fintiri, ya ce jama’a sun ki amincewa a kakaba musu shugaba, sun kuma kada kuri’a neman tazarcensa.
A wani batun kuma, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya taya gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri murnar sake lashe zabensa a karo na biyu.
Atiku Abubakar a wata sanarwa da ya fitar ya godewa al’ummar jihar Adamawa bisa sake zaben Ahmadu Fintiri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: