Ayayin da aka Kammala gudanar da al’amuran bikin tunawa da cikar Najeriya shekaru hamsin da tara (59) da samun ‘yanci kai, Sawaba FM tayi waiwaye domin nazarin wasu jerin mu’himman abubuwa guda goma sha daya (10) akan Najeriya da ya kamata duk dan kasa yasani.
Wadanda suka hadar da.
1 Najeriya ce kasa ta 32 a cikin jerin kasashen duniya da ke da girman -kasa, da ya kai fadin murabu’I 923,768.
2 Marigayi Benedict Odiase, mataimakin kwamashinan ‘yan sanda mai ritaya, Shi ne wanda ya kirkiri kidan taken Najeriya da ake amfani da shi a yanzu.
3 Mutane hudu ne suka hada kalmomin taken Najeriya, Mutanen dai sune Dakta Omoigui John Ilechwukwu, Eme Etim Akpan, B.A Ogunnnaike da P.O.
4 Akwai jami’o’in gwamnatin tarayya 37, da kuma 37 mallakar jihohi da kuma fiye da guda 50 masu zaman kansu.
5 Kididdigar jama’a ta karshe da aka yi a shekarar 2006 ta nuna cewa akwai mutane miliyan 140,431,790, Inda jihar kano ke kan gaba da yawan mutane sai kuma jihar legas da ta biyo bayanta, sai dai yanzu kiyasi ya nuna cewa akwai a kalla mutane 180,000,000 a Najeriya.
6 Najeriya ce kasa ma fi yawan jama’a a nahiyar Afrika, sannan kasa ta bakwai a yawan jama’a a duniya.
7 Flora Shaw, matar Lord Lugard, ita ce wacce ta kirkiri sunan Najeriya. Lord Lugard na daya daga cikin turawan da suka Mulki Najeriya a lokacin mulkin mallaka.
8 A ranar 1 ga watan janairu na shekarar 1901, Kasar Ingila ta mayar da Najeriya karkashin muliknta.
9 An yi yakin basasa mafi tsawo a Najeriya daga ranar 6 ga watan Yuli na shekarar 1967 zuwa watan janairu na shekarar 1970, Watanni 30 kenan.
10 Najeriya ta kasance a karkashin mulkin soji da farar hula har tsawon shekaru 33, tun daga shekarar 1966 zuwa 1999 daga bisani aka sami canjin mulki ta koma zuwa hannun farar hula zalla.
Tun bayan samun ‘yan cin kai, Najeriya ta samu jerin shugabanni har guda goma sha shida (16) wadanda daga cikin su 7 ne suka yi Mulki a matsayin sojoji sai kuma guda 6 da su kayi mulki a matsayin farar hula.
Sai dai Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Olusegun Obasanjo sunyi Mulki har sau biyu a matsayin soji da kuma farar hula.
Shugabanin da suka Mulki Najeriya sun hada da Dakta Nnamdi Azikwe. da Sir, Abubakar Tafawa Balewa, da Manjo Janar Johnson Thomas Aguiyi-Ironsi, da Janar Yakubu Gawon. da kuma Olusegun Obasanjo.
Bayan haka kuma sai Marigayi Alhaji shehu Usman Aliyu Shagari, sai kuma Muhammadu Buhari ya maye kujerar shehu Shagari, Sai kuma chief Earnest Shonekan, Daga bisani kuma Janar Sani Abacha ya zama shugaban kasa, wanda kuma Abdulsalam Abubakar ya biyo bayansa a matsayin shugaban kasa, Marigayi Umar Musa Yar Adua shi ne shugaba na gaba, Sai kuma Goodluck Elebe Jonathan, Inda kuma Muhammadu Buhari ya zama shugaba har zuwa yau din nan da muke ciki.