Abubuwa 5 da Ke Lalata Albashin Ma’aikata a Najeriya – Sanata Shehu Sani

0 552

Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana abubuwa guda biyar da ke lalata albashin ma’aikata a Najeriya.

Sanata Sani ya ce wadannan abubuwa guda biyar suna rage darajar albashi, musamman ma na kananun ma’aikatan kasar.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (@ShehuSani) yayin bikin ranar ma’aikata a ranar Alhamis, 1 ga Mayu, 2025.

Sanatan ya lissafa abubuwan kamar haka: Cire tallafi. Karin farashin wutar lantarki da na sadarwa. Tsadar farashin kayan masarufi (hauhawar farashi). Faduwar darajar Naira. Karin kudin haya.

Leave a Reply