Allah yayiwa Tsohon Shugaban Kasar Masar, Mohammed Morsi Rasuwa bayan faduwa da yayi a gaban kotu a Yau Litinin.

Kafar yada labaran Talabijin ta kasar Masar ta bayyana cewa Tsohon Shugaban kasar ya rasu ne yayin da ake zaman kotu don sauraron kararsa da ake yi.

Rahotanni sun ce ya suma ne a yayin zaman kotun inda ake tuhumarsa da laifukan cin amanar kasa, jim kadan bayan sumar tasa sai ya cika. Ya bar duniya yana da shekara 67.

Morsi Dai Sojoji ne suka Hambarar dashi bayan ya lashe zaben Kasar ta Masar a Shekarar Dubu Biyu da Sha Ukku a wani Yanayin Juyin Juya Hali.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: