Ku Kula da Takardun Shaidar Karatunku, Don Ba Sauyawa Har Abada- WAEC

0 149

A ranar Lahadi ne Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandire ta Afirka ta Yamma, WAEC ta shawarci mutnen da suke da Takardun Shaidar Karatun da take bayarwa da su yi kaffa-kaffa da su, domin kuwa ba za ta ƙara bada wasu ba idan suka ɓata, suka ƙone ko aka sace.

Shugaban Ofishin Hukumar na Najeriya, Olu Adenipekun ya bada shawarar a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa NAN a Legas.

Mista Adenipekun ya ce bada shawarar ya zama wajibi duba da yadda mutane da dama ke zuwa wajen Hukumar a lokuta daban-daban don a ƙara ba su Takardun Shaidar Karatunsu da suka ɓata.

“Bari in fito da abin fili cewa a gaskiyar magana, sau ɗaya muke bada Takardun Shaidar Karatun, ko wane ne kuwa, ko wane dalili ne ya jawo ɓatan, wannan kuma shi ne gaskiyar lamari.

“Ba ma bada Takardar Shaidar Kammala Babbar Sakandire ɗinmu ta Afirka ta Yamma sau biyu.

“Amma, idan aka samu dalilai kamar na sacewa, gobara, ambaliyar ruwa da sauran dalilai, kamar yadda ya shafi waɗannan Takardun Shaidar Karatu, e, idan muka yi la’akari da yadda muke gudanar da aiki, za mu iya bada Attestation Certificate.

“Shekaru biyar da suka gabata, Hukumar, wato sashi mafi girma na Hukumar suka yi taron ganawa, suka ɗauki mataki a kan haka, yana mai nanata cewa ba wata hukuma mai shirya jarrabawa dake ba ɗalibi ɗaya Takardar Shaida guda biyu a jarrabawa ɗaya.

“Amma, idan wani ɗalibi ya rasa Takardar Shaidar Karatunsa ta hanyar gobara, ambaliyar ruwa ko sacewa, kuma zai iya kawo dukkan hujjojin da suka zama wajibi da za su nuna lallai haka ne, waɗanda za su nuna lallai haka ta faru ga Takardar Shaidarsa ko Takardar Shaidarta, akwai wasu matakan da irin waɗannan ɗalibai ya kamata su ɗauka kafin su tunkari Hukumar don mataki na gaba”, in ji Mista Adenipekun.

Shugaban na WAEC ya ce bayan an gama bin dukkan waɗancan sharaɗai, Hukumar za ta duba yiwuwar bada Attestation Certificate.

“Wannan ita ce Takardar Shaidar da muke bayarwa, ba wai sake bada wata Takardar Shaidar Karatu ba.

“Wannan shi ne abinda muke yi a shekaru biyar da suka gabata.

“Muna da ‘yan Najeriya da yawa da suka amfana da wannan, saboda kamar maye gurbin Takardar Shaidar ne ta asali.

“Waɗannan mutane da suka amfana da wannan tsari sun zo ne daga dukkan ɓangarorin al’umma”, in ji shi.

A cewarsa, a ƙoƙarin rage yawan ɓatan Takardun Shaida da kuma bayar da kariya gare su, Hukumar a Najeriya ta shigo da abinda ta kira “Kare Takardar Shaida” shekaru biyar da suka wuce.

Ya yi bayanin cewa ɗaya daga cikin hanyoyin da ɗalibai ko mutane ke lalata Takardun Shaidar Karatunsu yawanci shi ne ta hanyar sa musu leda.

“An gano cewa da yawa daga cikin mutane sukan yi gaggawa zuwa shagunan masu Intanet da zarar sun karɓi Takardar Shaidar Karatusu na WASSCE, a ƙoƙarinsu na sa musu leda, a haka sai a lalata su”, a kalamansa.

Mista Adenipekun ya ce Takardun Shaidar Karatun Hukumar da ba a sa mugu gam ba babu irinsu, kuma suna da tsaro, ko da an tsoma su a cikin ruwa.

Ya ƙara da cewa waɗannan suna daga cikin sabbin abubuwan da Hukumar ta ɓullo da su a ‘yan shekaru don hidimta wa al’umma yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: