Adadin mace-macen zazzabin cizon sauro a Najeriya ya ragu da kashi 55 cikin dari

0 247

Daraktan shiyya na Hukumar Lafiya ta Duniya a Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ya ce adadin mace-macen zazzabin cizon sauro a Najeriya ya ragu da kashi 55 cikin dari.

Moeti ya bayyana haka ne jiya a yayin da yake kaddamar da rahoton zazzabin cizon sauro na Najeriya na shekarar 2022 a Abuja a babban taron da ministocin lafiya da walwalar jama’a suka yi tare da tawagar hadin gwiwa da babban daraktan asusun duniya da kuma ko’odinetan yaki da cutar kanjamau na Amurka a Najeriya.

Moeti ya kuma ce Najeriya ta samu ci gaba kan cutar kanjamau tsakanin shekarar 2015 zuwa 2021, inda ta cimma biyu daga cikin muradun kaso 95, kuma ana samun ci gaba a fannin kula da cutar tarin fuka, tare da kara gano masu dauke da cutar a lokaci guda. Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya ruwaito cewa, muradun kaso 95 na nuni ne da wasu tsare-tsare masu alaka da martanin da kasashen duniya ke yi kan cutar kanjamau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: