Kashim Shettima ya nanata kudurin gwamnatin su na kyautata jin dadin ‘yan Najeriya

0 279

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya nanata kudurin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na kyautata jin dadin ‘yan Najeriya a cikin shirye-shiryenta.

Shettima ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake kaddamar da rabon kayan abinci na Naira biliyan 5 da miliyan 1 da gwamnatin jihar Sokoto ta yi.

Shettima ya bayyana godiyar gwamnatin tarayya ga gwamnatin jihar Sokoto bisa tallafin motocin aiki ga jami’an tsaro.

Hakazalika, Shettima ya kuma yabawa kamfanin samar da siminti mai suna BUA Group da ke jihar, bisa tallafin motocin sintiri guda 10 ga jami’an tsaro.

Ya kuma yi kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu a jihar da su yi koyi da rukunin kamfanin BUA tare da tallafawa hukumomin tsaro.

A wani labarin makamancin haka kuma, Kashim Shettima ya  kaddamar da wata gadar sama dake unguwar Rijiyar Dorowa da gwamnatin jihar ta gina a kan kudi naira biliyan 5 da miliyan 3.

Tun da farko Gwamna Ahmed Aliyu ya ce an raba kayan tallafin ne domin a shawo kan matsalolin da jama’a ke fuskanta musamman talakawa a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: