Sama da mutane 2,100 ne suka mutu a girgizar kasa a kasar Moroko

0 353

Ma’aikatan agaji daga kasashen waje sun isa Moroko domin taimakawa takwarorinsu na kasar a aikin ceton wadanda girgizar kasa ta sanya suka makale a baraguzan gini ko tsaunukan da aka gagara isa.

Sama da mutane 2,100 ne suka mutu a girgizar kasar ta daren Juma’a. wani masanin girgizar kasa yayi gargadin cewa za’a cigaba da zirgizar kasar na tsawon makonni da watanni.

Remy Musa daraktan cibiyar lura da girgizar kasa na yankin turai da meditaraniya, ya sanar da kafar yada labarai ta Sky News cewa, kawo yanzu kasar ta girgiza sau 25 tun lokacin da girgizar mai karfin maki 6.8 ta soma.

Gwamnatin Moroko ta ce ta amince da taimakon gaggawar da kasashen Qatar, da Hadaddiyar daular Larabawa da Birtaniya da Sufaniya suka yi.

Daruruwan mutane na ta turuwa asibitico domin bada taimakon jini a Marrakesh, yayin da dama ke naman sararin da zasu yi jana’izar yan uwansu da suka rasu.

Wasu na kokarin samar da kaburburan ko-ta-kwana domin binne gawarwaki yayin da ake cigaba da aiki ceto. Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross na harsashen za’a dauki lokaci mai tsawo kafin kasa ta murmure da asarar data tafka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: