Akalla fursunoni dubu 1 da dari 536 ne ke jiran shari’a a cibiyoyin gyaran hali daban-daban da ke Jihar Kano.
Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya biya tarar wasu mata guda takwas ciki har da mata masu juna biyu da masu shayarwa tare da wasu mata hudu a gidan gyaran hali na Goron-Dutse domin su shaki iskar ‘yanci.
A cewar wani bayani daga mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya kai ziyarar ba zata zuwa cibiyar jiya domin ganin halin da fursunonin ke ciki da kuma gano hanyoyin da gwamnatin jihar za ta tallafa musu wajen jin daɗi da gyaran halinsu.
Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta cibiyoyin gyaran hali da kuma yin sauƙi ga fursunonin da ke zaune saboda aikata ƙananan laifuka.
Ya nuna damuwarsa kan yawan fursunonin da ke jiran shari’a, inda ya ce daga cikin fursunoni dubu 1 da dari 939 da ke cikin cibiyoyin, 382 ne kawai aka yanke wa hukunci, yayin da dubu 1 da dari 536 ke jiran shari’a. Gwamnan ya ce gwamnati za ta haɗa kai da bangaren shari’a domin hanzarta yanke hukunci shari’a ga fursunonin don rage cunkoso a cibiyoyin gyaran hali a fadin jihar.