Attajirin dan kasuwar nan da ya fi kowa kudi a Afirka Alhaji Aliko Dangote, ya bayar da Tallafin naira biliyan 15 domin manyan ayyukan ci gaba a jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote dake Wudil a jihar Kano.
Dangote ya sanar da wannan gudummawa a wajen bikin yaye dalibai karo na biyar da aka gudanar a ranar Asabar a Kano.
Ya bayyana cewa kudaden za su taimaka wajen aiwatar da tsarin ci gaban jami’ar na tsawon shekaru biyar domin ɗaukaka ta zuwa matakin duniya.
A cewarsa, daga cikin ayyukan da za a aiwatar akwai ƙirƙira da gina sababbin ɗakunan kwanan ɗalibai, gina ɗakunan gwaje-gwaje na injiniya, da kuma gina katafaren dakin kwamfuta na zamani da ke da haɗin intanet na awa 24 a kowace rana.
Sauran ayyukan sun haɗa da gina katafaren ginin Majalisar Jami’a (Senate Building) da kuma samar da damar aikin yi ga daliban da suka fi kwarewa bayan kammala hidimar kasa ta NYSC.
Dangote ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kokarinsa wajen magance matsalar yaran da ke zaune a gida ba tare da zuwa makaranta ba.
Ya bukaci masu hannu da shuni da su tallafa wa gwamnati domin sanya yara makaranta, yana mai cewa gudummawar jama’a na da matukar muhimmanci wajen ci gaban ƙasa baki ɗaya.