Akalla mutane 4 ne suka mutu a wani hadarin mota tsakanin wasu motocin haya guda 3 a jihar Sokoto

0 52

Akalla mutane 4 ne suka mutu a wani hadarin mota tsakanin wasu motocin haya guda 3 a jihar Sokoto.

Hakan ya haifar da zanga-zanga daga wasu fusatattun matasa wadanda suka cinna wuta kan wasu motaci biyu na hukumar hana fasa kwauri ta kasa (custom).

Fusatattun matasan sun dora alhakin hadarin da ya jawo asarar rayukan mutane 4 akan wajen binciken ababen hawa na hukumar kwastan dake shiryyar Asara a Illela.

Da yake mayar da martani, kakakin ofishin hukumar ta kwastan na shiyyar jihoshin Sokoto da Zamfara, Tahir Balarabe, ya bayyana lamarin da abin takaici.

Ya tabbatar da cewa fusatattun matasan sun kone motocin hukumar guda 2 tare da wata mota mallakin shugaban ofishin hukumar na Asara.

Tahir Balarabe ya nanata cewa jami’an hukumar na gudanar da ayyukansu ne kawai ta hanyar dakile fasa kwaurin lalatattun kayayyaki zuwa kasarnan, kamar yadda doka ta tanadar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: