Sama da mutum 50 da gawurtaccen dan fashin daji Bello Turji ya sace sun shaki iskar ‘yanci

0 91

Sama da mutane 50 da gawurtaccen dan fashin daji Bello Turji ya sace, sun shaki iskar ‘yanci.

Shugaban kwamitin kawo karshen fashin daji na jihar, Dr. Abdullahi Shinkafi, ya tabbatar da hakan ga manema labarai yau da safe.

Dr. Shinkafi yayi nuni da cewa wadanda aka sace sun kai 70, inda ya kara da cewa gawurtaccen dan fashin dajin ya sake su ba tare da wani sharadi ba, sanadiyyar lugunden wuta da ake yi akan sansanonin yan fashin daji dake dazukan jihoshin Zamfara da Sokoto.

Luguden wutar yayi sanadiyyar mutuwar wasu gawurtattun ‘yan fashin daji su 2, yayin da sauran suka samu munanan raunuka.

A cewar ‘yansanda, tuni aka kammala shirye-shiryen kwashe wadanda aka saki zuwa babban birnin jihar, Gusau, domin duba lafiyarsu kafin a mika su ga ‘yan’uwansu.

An rawaito cewa wannan cigaban ya kuma samu ne biyo bayan tattaunawar da aka yi tsakanin gawurtaccen dan fashin dajin tare da kananan hukumomin jihar Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: