Kungiyar RIFAN zata gudanar da bikin shinkafa da nufin tallafawa yunkurin gwamnatin tarayya na wadatar da abinci a Najeriya

0 20

Kungiyar manoman shinkafa ta kasa (RIFAN) na shirin gudanar da bikin shinkafa a Abuja da nufin tallafawa yunkurin gwamnatin tarayya na wadatar da abinci a kasarnan.

Ana sa ran za a gudanar da bikin a harabar cibiyar kasuwanci da masana’antu ta Abuja, kuma tuni aka yi nisa a shirye-shiryen samun nasarar bikin.

A wani batun kuma, hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta sanar da mutuwar karin mutane 6 sanadiyyar cutar corona tare da samun sabbin mutane 670 da suka harbu da cutar a jihoshi 10 na kasarnan da babban birnin tarayya.

Hakan na kunshe ne cikin bayanin da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook yau da safe.

Da sabbin wadanda suka harbu, yawan wadanda cutar ta yi ajalinsu a kasarnan sun kai dubu 3 da 45, yayin da jumillar wadanda cutar ta harba suka karu zuwa dubu 244 da 120.

Kamar yadda alkaluman na NCDC suka nuna, an sallami mutane dubu 216 da 180 bayan sun warke a fadin kasarnan, yayin da har yanzu mutane dubu 24 da 859 suke samun kulawar likitoci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: