Kwamitin Zakka ta masarautar Kazaure ta raba kayan abinci da kudinsu fiye da naira miliyan 17

0 101

Kwamitin Zakka na masarautar Kazaure yace ya raba kayan abinci da kudinsu ya kai naira miliyan 17 da dubu 671 da 500 ga mabukata dubu 3 da 646 a gundumomin Amaryawa da Dandi dake masarautar a wani bangare na kokarin rage yunwa tsakanin marasa galihu.

Shugaban kwamitin, Bala Muhammad Kazaure, ya sanar da haka lokacin da yake kaddamar da aikin rabon kayayyakin na bana a kauyen Todarya na gundumar Dandi.

Ya kara da cewa kayayyakin da aka raba sun hada da buhunan shinkafa 29 da rabi da na gero, dawa, masara, wake, da shanu da tumakai da awakai da sauransu.

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Najeeb Hussaini Adamu, wanda ya samu wakilcin Makaman Kazaure, Alhaji Jamilu Umar Adamu, yayi kira ga iyaye da su saka yayansu a makarantun boko da Islamiyya domin su amfani kansu tare da amfanar al’umma baki daya.

Sarkin ya bukaci a cigaban da addu’o’in samun zaman lafiya a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: