Ministan wutar lantarki, Engineer Abubakar Aliyu, yace za a iya samun karuwar wutar lantarkin kasarnan fiye da megawatt dubu 5 da za ake watsawa da rarrabawa idan aka aiwatar da ayyukan wutar lantarki da aka bayar na kudi naira miliyan dubu 43 da miliyan 750.

Wata sanarwa daga kakakinsa, Isa Sanusi, tace ministan ya mika takardun neman amincewa da ayyuka guda 16 wadanda majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da su kwanannan.

Ministan yace wutar lantarkin da ake da ita a yanzu ta kusa megawata dubu 5, inda ya nuni da cewa baza ta isa kasarnan ba, kasancewar manyan kalubalen suna wajen hanyoyin watsawa da rarrabawa.

Duk da kasancewar kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 suna hannu ‘yan kasuwa, kamfanin watsa wutar lantarkin TCN hukumar ce a karkashin ma’aikatar wuta ta tarayya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: