Gwamna Badaru ya wakilci shugaban kasa Buhari a wajen bikin rufe taron tarihi na wasan gargajiya na kasar Nijar

0 100

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen bikin rufe taron tarihi na wasan gargajiya na kasar Nijar karo na 42 da aka gudanar a birnin Yamai babban birnin kasar.

Gwamnan wanda ya jagoranci tawagar shugaban kasa ya samu tarba daga shugaban kasar Nijar Muhammed Bazaoum a fadar shugaban kasa dake birnin Yamai inda suka tattauna wasu batutuwan da zasu amfanar da kasashen biyu.

A lokacin ziyarar Gwamnan ya yi amfani da wannan dama wajen kara kulla alaka tsakanin Jamhuriyar Nijar da jihar Jigawa inda suka tattauna da ministan kasuwanci da masana’antu da ministan harkokin cikin gida da tawagar kungiyar tattalin arzikin Nijar domin bunkasa dangantakar tattalin arzikin jihar Jigawa da Nijar.

A wani labarin kuma, shugaban riko na hukumar raya yankin Neja Delta Effiong Akwa yace shugaban kasa Muhammadu Buhari baya neman alfarma daga wajen wadanda ya bawa mukaman siyasa.

Effiong Akwa ya fadi haka a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron kungiyar ‘yan jaridu ta kasa, reshen jihar Akwa Ibom.

Leave a Reply

%d bloggers like this: