Jam’iyar PDP ta Kasa reshen Jihar Zamfara ta bukaci Gwamnan Jihar Bello Matawallen Maradun, ya magance matsalolin tsaro da suke cigaba da addabar Jihar.

Da yake Jawabi ga Manema Labarai Mataimakin Shugaban Jam’iyar na Jihar Farfesa Kabiru Jabaka, ya ce cikin kwanaki 7, kimanin mutane 50 ne yan bindigar suka kashe a Jihar.

Da yake bayyana damuwar sa kan karuwar matsalolin tsaro a Jihar, Mataimakin Shugaban Jam’iyar  ya ce cikin Makonnan an yi Garkuwa da mutane masu tarin yawa.

Haka kuma ya zargi Gwamnatin Matawalle da gazawa wajen magance matsalolin da suke addabar Jihar musamman ta fuskar tsaro.

A cewarsa Farfesa Jabaka, kamata ya yi Gwamna Matawalle ya zauna a Jihar sa domin jajantawa mutane da hare-haren yan bindiga ya shafa maimakon tafiye-tafiyen marasa tushe.

Kazalika, ya ce Gwamna Matawalle bai iya gina koda aiki guda na cigaba a Jihar Zamfara ba. 

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: