Shugaba Buhari yace ba zai gaza ba wajen fara aiwatar da shirye-shiryen da suke cikin kasafin kudin Najeriya na 2022

0 88

Fadar Shugaban Kasa, ta ce shugaba Buhari ba zai gaza ba wajen fara aiwatar da shirye-shiryen da suke cikin kasafin kudin kasar nan na shekarar 2022, duk da sauye-sauyen da yan Majalisun kasa suka yi.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin sa Malam Garba Shehu, ya sanyawa hannu wanda aka rabawa manema labarai a Abuja a jiya.

Shugaba Buhari a ranar Juma’a ya sanya hannu kan kasafin kudin Kasar nan na shekarar 2022, sai dai ya bayyana damuwa kan yadda yan Majalisar suka sauya wasu daga cikin abubuwan da kasafin ya kunsa, wanda aka gabatarwa Majalisun.

Sai dai kwanaki biyu da kalaman shugaban Kasar, Kakakin sa Malam Garba Shehu, ya ce babu wani rashin Jituwa a tsakanin yan Majalisar da kuma Shugaban Kasa.

Sanarwar ta ce duk da sauye-sauyen da yan Majalisar suka yiwa kasafin kudin na shekarar 2022, hakan bazai shafi gwamnatin tarayya ba wajen aiwatar da kasafin kudin ba.

An bada rahotan cewa yan Majalisar sun sanya ayyuka Dubu 6 da 576 wanda kudin su yakai Naira Biliyan 37 a cikin kasafin kudin wanda hakan ya kawo musayar yawu a tsakanin bangarorin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: