Masu fafutukar kare mulkin demokradiyya a kasar Sudan zasu cigaba da sabbin zanga-zanga

Masu fafutukar kare mulkin demokradiyya a kasar Sudan sun sanar da sabbin zanga-zanga daidai lokacin da rikicin siyasa ya kara muni bayan murabus din Fira-Ministan Abdalla Hamdok a jiya.
Akalla masu zanga-zanga 3 aka kashe a ranar Lahadi bayan dubban masu zanga-zangar dake adawa da mulkin sojoji suka bazama kan tituna.
Adadin masu zanga-zangar da aka kashe tun bayan juyin mulkin sojoji na watan Oktoba ya karu zuwa 56.
Kungiyar kwararrun kasar Sudan, gamayyar kungiyoyin ma’aikata, dake jagorantar zanga-zangar adawa da mulkin sojoji, tace masu zanga-zangar zasu tunkari fadar shugaban kasa.
Shugaban kasar na mulkin soja, Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya gayawa jagororin soja a jiya cewa sojojine jigon tsaron kasar kuma zasu kare tsarin mika mulki ga fararen hula.
Jakadan majalisar dinkin duniya a Sudan, Volker Perthes, yace yayi takaicin matakin Abdallah Hamdok na yin murabus.