‘Har yanzu gwamnatin Najeriya bata ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda ba’ – Malami

0 86

Babban lauyan tarayya kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami, yace har yanzu gwamnatin tarayya bata ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda ba, saboda gwamnati tana koyi da sauran manyan kasashen duniya.

Yace ofishinsa yana kan aikin fara aiwatar da umarnin kotu da ya umarci gwamnati ta ayyana ‘yan fashin dajin a matsayin ‘yan ta’adda, inda ya kara da cewa nan da ‘yan kwanaki za a kammala aikin.

Abubakar Malami yayi magana a yau a matsayin bakon wani shirin gidan talabijin na NTA.

Mai shari’ah Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar 26 ga watan Nuwamban bara, ya bayar da umarnin ayyana ‘yan fashin daji da ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, amma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kasa aiwatar da umarnin sama da wata guda baya.

Da yake magana cikin shirin a yau, Abubakar Malami yace gwamnati ta gaggauta ayyana kungiyar IPOB da Boko Haram a matsayin kungiyoyin ta’adda saboda barazanar da suke yiwa rayuka da dukiya a kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: