ASUU bata da dalilin tafiya yajin aiki saboda mun biya – Gwamnatin Tarayya

0 72

Gwamnatin tarayya tace kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) bata da dalilin tafiya yajin aiki kasancewar ta biya dukkan bukatusn malaman dai-dai nauyin aljihunta.

Daraktan yada labarai da huldar jama’a na ma’aikatar ilimi ta tarayya, Ben Bem Goong, ya zanta da manema labarai lokacin da yake mayar da martani akan kalaman da aka ce shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, yayi na cewa kudaden da gwamnatin tarayya ta saki basu isa ba wajen magance kalubalen da jami’o’i suke fuskanta.

An rawaito Osodeke na cewa akwai yiwuwar kungiyar zata iya sake tafiya yajin aiki, har sai gwamnati ta magance mata bukatunta, ciki har da yarjejeniyar shekarar 2009.

Yayin da karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, yace babu wata hujjar da zata sanya kungiyar ASUU ta shiga wani yajin aiki, inda yace gwamnatin tarayya ta magance matsalolin da kungiyar ta lissafa, Ben Goong yace yajin aikin bashi da wani alfanu kasancewar ya fi lalata tsarin ilimin jami’o’in kasarnan fiye da cigaban da ya kawo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: