Yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutum 7 yan’uwan juna a kauyen Sabon Birni na jihar Kaduna

0 78

Yan bindiga dauke da makamai a jiya sun kashe wasu mutane 7 ‘yan’uwan juna a wani hari a kauyen Sabon Birni a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai yau da safe.

Samuel Aruwan yace akwai yiwuwar adadin wadanda suka mutu ya karu kasancewar jami’an tsaro dake aikin kwantar da tarzoma suna samun sabbin wadanda suka mutu.

Mazauna kauyen sun ce lamarin ya auku a jiya da dare lokacin da ‘yan bindigar suka mamaye kauyen da yawansu suka fara harbin kan mai uwa da wabi.

Wani jagoran al’umma, Bello Musa, ya gayawa manema labarai cewa mazauna kauyen dayawa sun arce daga gidajensu saboda fargabar hari ko kisa a hannun ‘yan fashin dajin.

‘yan bindigar sun kaddamar da makamancin wannan harin kan wasu kauyuka 13 a mazabar Kerawa a Karamar Hukumar Igabi, inda suka kashe akalla mutane 17.

Leave a Reply

%d bloggers like this: