Karin mutum 428 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya

0 65

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 428 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar ajiya Talata 4 ga watan Janairu 2022.

Daga cikin sabbin wadanda suka kamu da cutar jihar Rivers ke kan gaba da mutane 188 sai Ondo 54 sai babban birnin Najeriya Abuja mai 42 sai Imo 25 sai Nasarawa 24 sai Oyo 23 sai Edo 18.

Sauran su ne Akwa Ibom 16 Ogun 14 sai Osun 10 sai Kano 7 sai Ekiti mai 3 sai Borno mai mutum 2 yayin Filato ita ma take da 2.

Leave a Reply

%d bloggers like this: