Rundunar yan Sandan jihar Zamfara ta ceto fiye da mutum 90 da aka yi garkuwa da su a dajin Shinkafi

0 44

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta ceto akalla mutum 97 da aka yi garkuwa da su a dajin Shinkafi zuwa Tsafe a jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ayuba El-Kana ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Gusau ajiya Talata.

El-Kana ya ce an yi nasarar ceto mutanen ne sakamakon luguden wutar da jami’an tsaro ke yi a yankunan Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji, wadanda kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ya addaba.

A ranar 3 ga watan Janairu, 2022 ne jami’an tsaro suka samu labarin ganin wasu mutane da ake zargin sace su aka yi a cikin dajin da ke yankin Shinkafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: