Gwamnatin tarayya ta gudanar da aiyukan hanyoyi 974 masu nisan kilomita dubu 13 cikin shekaru 6

0 58

Gwamnatin tarayya ta gudanar da aiyukan hanyoyi 974 masu nisan kilomita dubu 13 cikin shekaru 6 da suka gabata.

Babban sakataren ma’aikatar ayyuka da gidaje na kasa Babangida Hussaini ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja, inda yace aiyukan na daga cikin alkawarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na bunkasa tattalin arzikin kasarnan.

Yace duk da kalubalaen tattalin arziki da gwamnatin tarayya ke fuskanta, ta gudanar da manyan ayyuka kari bisa gyaran hanyoyi na biliyoyin naira, da ta gudanar a shiyoyin kasarnan.

Babangida Hussain ya kara da cewar za a kaddamar da aikin hanyar Abuja-Kaduna-Zaria-Kano a watan uku na wannan shekara yayin da aka mika aikin hanya, da gadar Shuwarin-Azare ga gwamnatin jihar Jigawa.

Babban sakataren ya ta’allaka jinkirin da ake samu na kammala aikin hanyar Kano-Katsina akan rashin biyan kudaden diyya da cire turakunan lantarki dake kan hanyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: