Kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra ta haramta yin taken Najeriya da cin naman shanu a yankin Kudu

0 102

Kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB, ta haramta yin taken Najeriya da cin naman shanu a wuraren bukukuwa da daukacin makarantun da ke kudu maso gabashin kasarnan.

A cikin wata sanarwa da aka fitar jiya ta hannun sakataren yada labaranta, Emma Powerful, kungiyar tace dokar zata fara aiki daga watan Afrilu mai zuwa.

Sai dai, kungiyar ta IPOB bata sanar da ranar fara aiki da dokar haramta rera taken Najeriya ba.

Emma Powerful wanda yaki cewa uffan dangane da matakan da za a dauka na tabbatar da kiyayewa da dokokin, yace duk makarantar da aka samu ta karya dokar za ta yi dana sani.

Kungiyar ta IPOB ta kuma musanta rahotannin dake cewa kungiyar tsaro ta ESN tana da hannu a kashe-kashe da sace-sacen mutane da ake yi a yankin na Kudu maso Gabas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: