Hukumar kula da yawon bude ido ta jihar Bauchi ta ce za ta horar da ma’aikatan gandun daji guda 350 domin inganta kariya da tsare namun daji.

Babban Manajan Hukumar Malam Nasir Yusuf ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Bauchi.

Nasir Yusuf ya ce horon na kwanaki uku, wanda za ayi bisa kulawar wasu da aka zabo daga hukumomin tsaro na gwamnati da masu zaman kansu za a gudanar da shi cikin wannan watan.

Ya ce za ayi horon ne da nufin ilimintar da mahalarta kan wasu ka’idojin tsaro na kare dabbobi daga barazana.

Hukumar, in ji shi, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare nau’ikan dabbobi daban-daban guda 139 da ake da su a wuraren shakatawa da Gandun daji a fadin jihar.

A cewarsa, hukumar za ta shirya irin wannan horon ga shugabannin al’umma kan kariya da adana wuraren yawon bude ido da kayayyakin tarihi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: