An gano yaran Fulani su dubu 49 da 712 da ba sa zuwa makaranta a jihar Jigawa

0 119

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce kawo yanzu ta gano yara Fulani su dubu 49 da 712 da ba sa zuwa makaranta a fadin jiharnan.

Sakatariyar hukumar kula da ilimin makiyaya ta jihar Jigawa, Hajiya Ramatu Muhammad ce ta bayyana haka a lokacin da take tilawar ayyukan hukumar a cikin wani shiri na gidan rediyon Jigawa.

Ta ce sakamakon kidayar da hukumar ta gudanar watanni uku da suka gabata ya nuna cewa sama da yara dubu 49 da 712 da ba sa zuwa makaranta aka samu a kauyuka da rugagen Fulani 366 da ke jiharnan.

Ramatu Muhammad ta ce gwamnatin jihar Jigawa tana iya bakin kokarinta wajen ganin an kara kusantar da ilimi ga kauyuka da rugagen Fulani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: