Wasu yan daba dauke da makamai sun kai farmaki wani ofishin gidan jarida a jihar Zamfara

0 103

Wasu ‘yan daba dauke da makamai sun kai farmaki zuwa ofishin jaridar internet da gidan talabijin na Thunder Blowers Online dake Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

An gano cewa maharan sun tunkari ofishin a ranar Litinin da dare, inda suka raunata edita, Mansur Rabi’u, tare da lalata wasu kayayyakin aiki.

Cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Zaharaddeen Zarumi, a madadin hukumar gidan, kafar yada labaran tace maharan sun bayyana cewa an aiko sune domin koyawa daya daga ma’aikatan hankali.

Sai dai, sanarwar ta bayyana cewa hukumar bata da masaniyar wanda ya aiko da maharan.

Kakakin yansanda na jihar Zamfara, Mohammed Shehu, bai amsa wayarsa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: