Akalla mutane 5 aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu bama-bamai sun fashe a kusa da filin jirgin saman Maiduguri

0 67

Akalla mutane 5 aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu bama-bamai sun fada a kusa da filin jirgin saman Maiduguri kimanin sa’a daya kafin isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar Borno a wata ziyarar aiki.

Bama-baman da ake kyautata zaton an harba su ne daga wajen birnin sun fara sauka a wurare daban-daban a kusa da filin jirgin da misalin karfe 10 da mituna 45 na safe.

Shaidu da majiyoyin tsaro da ke da masaniya kan lamarin sun tabbatar da cewa akalla wasu bama-bamai guda biyar ne suka fado a galibin wuraren da jama’a ke zaune, lamarin da ya yi sanadiyar asarar rayuka da jikkata fararen hula da dama.

Wata majiya da ta zanta da manema labarai ta ce daya daga cikin bama-baman ya fado ne a unguwar Ayafe da ke wajen Ngomari, inda ya kashe mutane hudu ciki har da wata budurwa ‘yar shekara 16.

Wasu bama-bamai sun fada a Ajilari Cross, Moromti da kuma rukunin gidajen Legacy da ke Bulumkutu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: