Gwamnatin jihar Jigawa ta sake bada gudunmawar mota kirar Toyota Hilux ga rundunar yansanda ta jiha

0 53

Gwamnatin jihar Jigawa ta sake bada gudunmawar mota kirar Toyota Hilux ga rundunar yansanda ta jiha.

Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini ya mika makullan motar ga kwamishinan yansanda na jiha

Sakataren gwamnatin wanda ya samu wakilcin babban sakataren sashen tsaro da kuma majalissar zartarwa ta jiha Alhaji Abba Makama, yace hakan na daga cikin kudirin gwamnatin jiha na kara kyautata alamurran tsaro

Yace karin motar zai baiwa yansanda damar cigaba da gudanar da aiyukansu na kare rayuka da kuma dukiyoyin alummar jihar nan

A jawabinsa kwamishinan yansanda na jiha CP Aliyu Saleh Tafida ya yi alkawarin yin cikakken amfani da motar kari bisa wadanda gwamnatin jiha ta baiwa rundunar wajen kare rayuka da kuma dukiyoyin alummar jihar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: